1 Afirilu 2026 - 11:59
Source: ABNA24
Jagora: Tarihin Gwagwarmaya Cike Ya Ke Da Kwamandoji Masu Tsayin Daka Da Sadaukarwa

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Tura Saƙo Zuwa Ga Sheikh Naeem Qasim, Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A wani sako ga Sheikh Naeem Qasim, Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah a kasar Labanon, Jagora Ayatullah Sayyid Imam Mujtaba Husaini Khamenei ya yaba da nuna girmamawa da nuna kauna ga jagora da kuma nuna alhininsa da juyayin ta'aziyyar shahadar jagora mai girma. Da kuma nuna kauna da sadaukarwar mujahidan mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon. 

A cikin wannan sakon, Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa, Dakewa da tsayin daka kan manyan makiya na Musulunci, wato Amurka da gwamnatin Sahayoniya, na daya daga cikin fitattun siffofi na shahid jagoran juyin juya hali. 

Ayatullah Khamenei ya yi nuni da cewa tarihin gwagwarmayar Musulunci yana cike da gwagwarmaya da jajircewa da sadaukar da kai; Inda kwamandojin masu tsayin daka suka sadaukar da rayukansu don kare al'ummar musulunci ba tare da tsoron wata barazana ba.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha