Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wannan adadin ya karu bayan da a satn da ya gabata adadin ya kasance 200 kamar yadda majiyar cibiyar tsaron Amurka ta fada wanda hakan ma bayan ragewa tare da boye asalin adadin sojojin da yakin ya shafa ne
idan bamu manta ba a ranar Alhamis da ta gabata Iran ta harbo wani jirgin yakin Amurka kirar F35 wanda har yanzu ba su fadi yanayin asarar da aka haifar a jirgin ba' sannan akwai jirgin shima kirar KC135 wanda y fado ko kuma Iran ta harbo shi a ranar 12 ga watan nan wanda an tabbatar da mutuwar dukkan mahaya jirgin.
bugu da kari ga sojojin 7 da suka mutu da cibiyar tsaron Amurka ta bayar da rahotonsu bayan an kai harin kan sansanin da suke dukka wadannan adadin na karya ne domin adadin yafi haka amma Iran na ci gaba da kai hare-haren kariyar kai tun daga ranar da Amurka d Isra'ila suka fara kai ma ta hari watau ranar 28 Fabrairun da ya gabata.
Your Comment