Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Tare da goyon bayan al'ummar Iran da suka kasance Ako yaushe a fage wanda a daren yau sun fito kwansu da kwarkwatarsu ƙarƙashin ruwan sama, suna masu kafa tarihi juriya a yakin da ke faruwa.
A cikin wannan aiki, wanda aka gudanar da ramzin suna mai tsarki na: (Ya Dalilal Mutahayyiriin), tare da sadaukar da shi ga mutanen yankin gabashin kasar, ciki har da Kurasan ta Arewa, Razavi, Kudancin Sistan da Baluchestan.
A cikin wannan harin, an kai hari kan wurare Eilat da Dimona da arewacin Tel Aviv da wasu sansanonin sojojin ta'addanci na Amurka a yankin inda suka fuskanci mummunan hare-hare bisa amfani da makamai irinsu Emad da Qadr da ke ɗauke da kawunan yaƙi da dama jiragen yaƙi marasa matuka masu lalata komai suka kai hari kan shi.
Jami'an tsaron juyin juya hali tare hare-haren a fagen yaƙi suna ci gaba da kai hari a matsayin tattaunawa tare da masu aikata laifukan ta'addanci na Amurka da Isra'ila masu kashe yara.
Manyan rukunin yaki na dakarun juyin juya hali da kuma miliyoyin dakarun Basij har yanzu ba su shiga fagen fama ba, za su shiga ne yayin buƙatar hakan ta taso.
Makircin makiya don rama rashin cin nasararsu da canza ma'auni na yakin a cikin sa'o'i masu zuwa ba a boye su ke ga idanun dakarun juyin juya hali ba. Dakarun Iran zasu kai harin halakarwa ga masu aikata laifuka da mabiyansu a duk wani mataki na zalunci da aikata laifuka.
Ra'ayinka