Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A Farautar Tankunan yaƙi Merkava na Isra'ila Hizbullah ta sanar da cewa ta kai hari kan wata tankar Merkava a yankin Tayyiba da makami mai linzami. Don haka zuwa yanzu jimillar tankunan da ta kaiwa hari tun daren jiya ya kai tankuna 5.
Ali Shoaib, tsohon ɗan jarida Al-Manar Lebanon, ya sanar da buga wannan hoton cewa gwagwarmayar Hizbullah ta lalata tankunan Merkava na Isra'ila 16 ya zuwa yanzu.
Sannan Hizbullah ta ce: Mun kai hari da jiragen yaƙi marasa matuka kan wuraren radar da dakunan sarrafawar yaƙi na Ramat David Air Base.
Ra'ayinka