Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Lebanon ta sanar a cikin sanarwarta ta hudu a safiyar yau Laraba da karfe 3:30 cewa, a matsayin martani ga hare-haren keta iyaka na Isra'ila akan da yawa daga biranen Lebanon da yankuna da dama takai hari da makami mai linzami hedkwatar Rundunar Sojojin Isra'ila ta Arewa a Safad.
Sannan Hizbullah ta kai hari kan Cibiyar kere kere da sansanin jiragen yakin Isra’ila hakan yazo a cikin wata sanarwa mai namba biyu da kungiyar ta fitar. Inda ta ce: Mujahidan gwagwarmayar Musulunci sun kai hari kan hedkwatar kamfanin masana'antar sufurin jiragen sama na Isra'ila (IAI) da ke tsakiyar Falasdinu da aka mamaye da jiragen kunar bakin wake da karfe 2:00 na safiyar yau (Laraba).
Hizbullah ta kuma sanar a cikin sanarwar ta na uku cewa da karfe 03:30 na safiyar yau, ta kai hari kan sansanin kula da jiragen sama na GIFA da ke gabashin birnin Safad da aka mamaye da makami mai linzami. Kungiyar Hizbullah ta kai hari a hedikwatar arewacin Isra'ila.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da wata sanarwa da ta bayyana cewa, ta kai hari kan hedikwatar yankin arewa na sojojin abokan gaba sahyoniyawa da ke sansanin (Dadoo) da makami mai linzami.
A sabon harin makami mai linzami na kungiyar Hizbullah a arewacin Falasdinu ta sanar da kai hare-hare 13 akan yan mamaya a ranar Talata tare da sanar da sake kai hari a safiyar yau laraba. Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Lebanon ta sanar da cewa, ayyukan na ranar Talata sun hada da kai hari kan sansanoni, wuraren tattaruwar sojoji da kayan aikin sojojin sahyoniya, da tinkarar ta'addancin abokan gaba a kan iyakokin, da kuma harbo wani jirgin UAV a saman Nabatieh.
A cikin wani aiki na baya-bayan nan da aka kai a safiyar yau, kungiyar Hizbullah ta ba da rahoton wani hari makami mai linzami a wurin da sojojin Sahayoniya suka tattaru yankin Mutla tare da fitar da sanarwa da ta bayyana cewa, bisa mayar da martani ga ta’addancin gwamnatin Sahyoniya da ta yi akan da dama daga birane da garuruwan Lebanon, ciki har da Yankin kudancin Beirut, karfe 1:20 A safiyar yau Laraba, 4 ga Maris, 2026, mun kai hari wurin taron sojojin abokan gaba na sahyoniya a Al-Mutla tare da gungun makamai masu linzami.
Ita ma anata bayanin Tashar Isra'ila ta 12 ta ce: Kungiyar Hizbullah ta harba makamai masu linzami 30 a Isra'ila a daren jiya. A cikin kasa da mintuna 45, kungiyar Hizbullah ta luguden wuta akan Falasdinu ta Arewa hari sau hudu.
Hizbullah ta kuma sanar da kai hari kan sansanin sojojin ruwa na Haifa na Isra'ila. Sannan Hizbullah ta kuma sanar da cewa, ta kai hari kan wata tankar Isra'ila a yankin Al-Mutalla da makami mai linzami. Wanda kafofin yada labaran Isra'ila suka tabbatar da kai harin, suna cewa kungiyar Hizbullah ta kai hari a yau da makami mai linzami.
Hizbullah ta kuma sanar da cewa, ta yi wa dakarun Isra'ila ruwan rokoki da dama a tsaunin Al-Ajal da ke arewacin garin Kafrifal; Bayan nan Kungiyar Hizbullah ta sake harba wasu sabin makamai masu linzami tana mai caskala arewacin Isra'ila da makami mai linzami na Fadi 6.
Zuwa yanzu Hizbollah ta tarwatsa tankokin Merkava guda shida A yau da karfe 112 na rana, Hizbullah ta kai hari kan wata tankar Merkava a ƙauyen Hula da makamin da ya dace wanda adadin tankokin da aka lalalata sun shida zuwa yanzu.
Sannan Kungiyar Hizbullah ta fitar da bidiyon wasu hare-haren da ta kai a jiya kan sansanonin abokan gaba na Sahayoniya a arewacin Falasdinu wanda yake kunshe acikin wannan rahotanni.
Your Comment