1 Maris 2026 - 06:46
Source: ABNA24
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayi Shahada

Inna lillah Wainna Ilaihi Rajeuun  Babban jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi shahada a wurin aikinsa a gidansa an sanar da kwanaki 40 na zaman makokin jama'a da kwanaki 7 na hutun jama'a a kasar,

Kafofin yada labaran da ke da alaka da gwamnatin sahyoniyawan da kuma martanin yankin sun sha da'awar cewa yana ɓoye a wani wuri mai aminci da sirri saboda tsoron kar a kashe shi amma sai gashi yayi shahada a gurin aikinsa. 

Shahadarsa a wurin aiki ya sake tabbatar da rashin gaskiyarsu na waɗannan ikirari da yaƙin tunani na abokan gaba, kuma ya nuna cewa koyaushe jagora yana cikin al'umma yana tare da su a cikin ƙaƙƙarfan yanayi da rashin tsoro da ƙarfin hali. Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun fitar da bayani kamar haka: 

Da sunan Allah, Mai rahama, mai jin kai, kada kuyi tsammanin cewa wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne sai dai su rayayyu ne a wajen ubangijinsu ana masu azurtasu. 

بسم الله الرحمن الرحیم

ولاتحسبن الذین قتلوا فی سبیل الله امواتا بل احیاء عند ربهم یرزقون

Shahadar daukaka ta masanin ubangiji shugaban shahidai jagoran juyin juya halin Musulunci shugaban masu jiran bayyanar Imamul Mahdi Ajjalallahu Ta'ala Farajahush Imam Khamenei, Rizwanillahi Alaihi a watan Ramadan mai albarka.

Muna mika ta'aziyya rashinsa ga limamin zamani Rayukanmu fansa gareshi da Al'ummar Musulmi da manyan maraji'ai da malamai da babbar al'ummar Iran. 

Allah Madaukakin Sarki ya karbi wannan ruhin Mujahidai mai girma ta hanyar shahada kamar abin koyi da Amiril Muminina Alaihissalam a cikin watan Ramadan mai alfarma. 

Mun yi rashin babban jagora kuma mun zauna cikin makoki a gare shi, wanda ya zamo a cikin tsarkin rai, ƙarfin imani, dabara a cikin al'amura, jarumta a gaban masu girman kai ta hanyar yin jihadi a tafarkin Allah wanda ya zamo babu kamarsa a zamaninsa. 

Yayi Shahada a hannun mafi rabon 'yan ta'adda da masu kisan ƴan adama da mutuntaka alama ce ta halacci da gaskiyar wannan babban jagora da kuma karbuwar hidimominsa na gaskiya. 

Shahada a tafarkin musulunci da Iran mafi girma alama ce ta nasara da kusantar manufa; Sai dai shahadar da komawa zuwa ga Allah da Imam Khamenei Ridwanullahi Ta'ala alaihi ya yi tafarkinsa da hanyarsa ba zai tsaya ba kuma zai ci gaba da cikin karfi da daukaka. 

Wannan shahadar za ta kara sanya al'ummarmu maida hankali da kara azama wajen ci gaba da tafarkin haske na masoyinmu Imam Khamenei. Ayyukan ta'addanci na masu laifin ta'addanci na mugayen gwamnatocin Amurka da Sahayoniya sun saba wa ka'idojin addini, ɗabi'a, shari'a da na al'ada; 

Don haka hannun ramuwar gayya na al'ummar Iran mai tsanani ne domin hukunta su hukunci mai tsanani mai sanya nadama ga makasa limamin al'ummar ba zai bar su ba. Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci, da rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci, da kuma babban rundunar al'umma, za su ci gaba da kare tarihi mai daraja na wannan jagora mai girma, kuma za su yi tsayin daka wajen yaki da makircin ciki da waje tare da hukunta Masu Kai hari kasar Musulunci. 

A ƙarshe, muna gayyatar duk sassan al'umma don nuna juyayi da alamun haɗin kai da ga al'ummar duniya da mugaye da abokan gaba na ta'addanci na wannan al'umma tare da ƙwazo na ban mamaki a cikin fagen tsaron ƙasa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha