Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An kashe akalla mutane 33 a hare-haren 'yan bindiga a lokaci guda a arewa maso yammacin Najeriya. 'Yan sanda sun ce hare-haren sun faru ne a ranar Laraba a yankin Bio na jihar Kebbi.
Kakakin 'yan sanda Bashir Usman ya ce maharan sun shiga yankin daga makwabciyar jihar Sokoto, wanda wasu sassansa ke karkashin tasirin kungiyar Lakurawa. A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa 'yan bindigar sun shiga yankin da nufin satar dabbobi kuma an tura jami'an tsaro don dawo da zaman lafiya.
Kungiyar Lakorawa tana aiki a sassan arewa maso yammacin Najeriya kuma an san ta da kai hare-hare a kauyuka, sace-sacen mutane don fansa da satar shanu. Yankin arewacin kasar ya fuskanci matsalar tsaro mai sarkakiya a cikin 'yan shekarun nan, inda 'yan bindiga da kungiyoyin 'yan daba masu dauke da makamai suke yawaita sace-sacen mutane da haifar da tashin hankali.
A halin yanzu, Najeriya ta kara karfafa hadin gwiwa da Amurka don yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai. Rundunar sojin ƙasar ta sanar da isowar sojojin Amurka 100 kwanan nan don horar da sojojin Najeriya wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
……………………………………………………………
Your Comment