Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: an gudanar da wani taro na musamman mai taken taken "Bayyanar Mai Ceto Da Akai Alkawari A Karshen Zamani Daga Mahangar Addinai Da Makarantun Tunani Daban-Daban" a Tanzania, inda aka tattaro shugabannin addinai, malamai, da masu fafutukar zaman lafiya don tattaunawa mai zurfi kan daya daga cikin muhimman batutuwan tauhidi a tarihin dan adam.
An shirya wannan taron ne a karkashin jagorancin reshen Jami'ar Al-Mustafa ta kasa da kasa ta Tanzania, tare da hadin gwiwar Hukumar Sulhu da Zaman Lafiya ta Tanzania. Manufar taron shi ne inganta zaman tare na addini da kuma fadada tattaunawar ilimi kan imani da aka yi a kan mai ceto da Allah Ya yi alkawarin zuwansa a tsakanin al'adun addinai daban-daban.
Your Comment