14 Janairu 2026 - 22:04
Source: ABNA24
Za'a Fara Gundanar Da Kashi Na Biyu Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza

Steve Witcaf, wakilin shugaban Amurka a Gabas ta Tsakiya, yayin da yake sanar da fara kashi na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, ya yi kira ga Hamas da ta yi cikakken riko da wannan mataki.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyoyin Falasdinu bayan kammala taron kolin Alkahira: Muna bin dukkan sassan yarjejeniyar har zuwa aiwatar da dukkan matakanta. 

Muna kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa Isra'ila lamba da ta dakatar da ta'addancinta. 

Isra'ila na kokarin zagon kasa don hana aiwatar da kashi na biyu na tsagaita bude wuta a Gaza kamar yadda majiyoyin Falasdinawa suka ba da rahoton cewa, gwamnatin Sahayoniyya na yin zagon kasa ga zartar da mataki na biyu na shirin Amurka da tsagaita bude wuta a Gaza. 

Wasu majiyoyin Falasdinawa sun kuma bayar da rahoton cewa, gwamnatin Sahayoniyya na adawa da sake gina zirin Gaza da janye dakarunta daga yankin, wanda hakan wani cikas ne ga aiwatar da kashi na biyu na shirin Trump mai mataki 20; A halin da ake ciki, Trump ya yanke shawarar sanar da aiwatar da wannan shiri da sabon tsarin gwamnatin Zirin Gaza. 

A daya bangaren kuma, wasu jami'an Isra'ila da na yammacin duniya da manazarta sun soki matakin kashi na biyu na shirin Amurka kuma yin la'akari da shi a matsayin lamari da ya kasance nesa da hakikanin siyasa da tsaro na Gaza.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha