22 Nuwamba 2025 - 18:15
Source: Almanar
Sojojin Mamaye Suna Sake Kutsawa Yankuna Da Suka Janye Bayan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta.

A rana ta 43 da tsagaita wuta a Gaza, yankunan gabashin birnin Gaza na fuskantar sabon tashin hankali, bayan da aka tilasta wa iyalai da dama barin unguwannin Al-Tuffah da Al-Shuja'iyya bayan wani hari da sojojin mamaye suka kai musu da kuma faɗaɗa kasancewar dakarunsu zuwa yankunan da suka janye daga cikinsu a baya bisa ga yarjejeniyar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin mamaye sun kuma aikata aikin rushe gidaje masu yawa a tsakiyar yankin Gaza, a yankin arewa maso gabashin sansanin 'yan gudun hijira na Al-Bureij.

Wadannan ayyukan rusau sun gudanar lokaci ɗaya da harba manyan gurneti da manyan bindigogi daga tankunan yaƙi da jiragen sama na Isra'ila da ke gabashin Khan Younis da Rafah.

Kamar yadda tashar Almanar tace suna ci gaba da bin diddigin sabbin take hakki da Isra'ila ta ke yi a yankin Gaza tare da abokin aikinsu Imad Eid.

Your Comment

You are replying to: .
captcha