Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hajj Afif ya ɗauki nauyin hulɗar kafofin watsa labarai na Hizbullah sama da shekaru goma kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen bayyana saƙon gwagwarmayar Musulunci tare da daidaitonsa, ingantaccen bincike, da kuma wayar da kan jama'a game da ra'ayoyin gwagwarmaya.
Ya kuma yi bitar tarihin gwagwarmaya da 'yancin kai na Lebanon inda ya jaddada cewa 'yanci da gwagwarmaya ya samu ne sakamakon juriya da sadaukarwa da ƙoƙarin da al'ummar Lebanon da shahidai suka yi ne.
Sheikh Naim Qassem: Hizbullah Ita Ce Mai Kare Haƙƙin Lebanon
Sakataren Hizbullah a Lebanon ya jaddada cewa ƙungiyar ta yi imani da cikakken 'yancin kai na ƙasar da kuma aiwatar da ikon mallaka a kan dukkan yankunan Lebanon, ba tare da wani dogaro ko wasu al'umma ba. Ya ƙara da cewa Hizbullah da al'ummar Lebanon ba za su bar ko da inci ɗaya na yankin ƙasar ya ci gaba da kasancewa ƙarƙashin mamayar gwamnatin Isra'ila ba.
Sheikh Qassem ya kuma yi ishara da cewa an ƙirƙiri gwagwarmaya ne don fuskantar mamayar kuma ba za ta miƙa Lebanon ga abokan gaba ba, kuma sabanin ikirarin Amurka na shiga tsakani Ita Amurka abokiya ce kai tsaye ce a cikin aikata ta'addanci.
Your Comment