Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Cibiyar Likitoci ta Sudan ta sanar da cewa akalla mutane 12 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a hare-haren da Rundunar gaggawa ta Kaiwa Sansanonin 'Yan Gudun Hijira a kwanan nan a Kudancin Kordofan.
A danagne da haka, Mani Arko Manawi, gwamnan yankin Darfur, ya jaddada cewa sojojin Sudan za su ci gaba da fafatawa har sai sun kwato yankunansu gaba daya.
Rundunar RSF ta yi amfani da jirgin sama mara matuki don kai hari ofishin Kungiyar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Duniya da ke birnin Kadu Qoli, inda ta kashe yara biyar. Haka kuma, wani hari da aka kai kan sansanin 'yan gudun hijira a yankin Al-Abbasiyah na Kudancin Kordofan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai, ciki har da mata da yara, wasu kuma da dama sun jikkata.
Dubban fararen hula ne suka rasa matsugunansu bayan faduwar birnin El Fasher, babban birnin jihar Arewa ta Darfur, Wael Mohamed Sharif, kwamishinan jin kai na jihar Arewa, ya ce ana sa ran adadin mutanen da suka rasa matsuguninsu zasu isa jihar cikin awanni 48 masu zuwa.
Ya ce ana ci gaba da kokari sosai don biyan bukatun wadannan mutane. A cewar hukumomin yankin, birnin Dabbah ya riga ya karbi bakuncin mutane sama da 4,000 da suka rasa matsuguninsu daga Darfur da Kordofan.
A halin yanzu, sojojin Sudan sun sanar da cewa sun kai hare-hare ta sama kan sansanonin Rundunar RSF a Arewa da Yammacin Kordofan. A cikin wani sakon bidiyo a Facebook, Manawi ya bayar da rahoton ikirarin da Abdel Rahim Daqlo, mataimakin kwamandan Rundunar RSF, ya yi na cewa za a yi adalci kan laifukan da aka aikata a El Fasher.
Ya kamata a lura cewa birnin El Fasher, wanda shi ne sansanin karshe na sojojin Sudan a yankin Darfur, yanzu haka yana karkashin cikakken ikon Rundunar RSF. A bisa kiyasin Majalisar Dinkin Duniya, dubban fararen hula ne suka rasa matsugunansu tun bayan faɗuwar birnin, inda da yawa suka yi gudun hijira a garin Tawela, mai nisan kilomita 70 daga El Fasher, wani birni da a da ya dauki nauyin kimanin mutane 650,000 da suka rasa matsugunansu.
Yayin da rikicin jin kai a Sudan ke ƙara ta'azzara kowace rana, yaƙin da ke tsakanin sojojin ƙasar da Rundunar RSF ya fara ne a ranar 15 ga Afrilu, 2023, kuma ya ci gaba duk da ƙoƙarin shiga tsakani na yanki da na ƙasashen duniya.
Your Comment