Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Memba din ya fadi hakane a wani taron siyasa a garin "Ain al-Souda" da ke yammacin Baalbek: "Mutanen Lebanon A Yau Suna Tare Da Gwagwarmaya Ne Fiye Da Kowane Lokaci. A da, wasu suna shakkun goyon baya ko adawa da gwagwarmaya, amma yanzu, bayan hare-haren gwamnatin Sahyuniyawa, suna goyon bayan gwagwarmaya da makamanta".
Al-Miqdad ya kuma yayi ishara da hare-haren sama na Isra'ila kwanan nan a yankunan Bekaa da kudancin Lebanon, musamman garin "Shamstar," da cewa: wani sabon laifin ta’addanci ne kan fararen hula wanda ya haifar da tsoro da razani a tsakanin ɗalibai, ya raunata wasu daga cikinsu, kuma ya lalata makarantu.
Your Comment