16 Oktoba 2025 - 21:51
Source: ABNA24
Yaman Ta Tabbatar Da Shahadar Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar

Rundunar sojin Yaman ta sanar da shahadar babban hafsan hafsoshin kasar Manjo Janar Mohammed Abdul Karim Al-Ghamari a wani harin da Isra'ila ta kai a watan da ya gabata tare da wasu abokan aikinsa da dansa Hussein mai shekaru 13.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar sojin Yaman ta sanar da shahadar babban hafsan hafsoshin kasar Manjo Janar Mohammed Abdul Karim Al-Ghamari a wani harin da Isra'ila ta kai a watan da ya gabata tare da wasu abokan aikinsa da dansa Hussein mai shekaru 13.

A cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talbijin a yau Alhamis, sojojin sun sanar da shahadar Manjo Janar Al-Ghamari yayin da yake gudanar da aikinsa na nuna goyon baya ga Falasdinu. Sanarwar ta bayyana shi da abokan aikinsa a matsayin mayaka masu tsayin daka wajen tabbatar da manufarsu, masu zurfin ilimi da gogewa.

Duk da asarar da aka samu, Rundunar Sojin Yaman ta tabbatar da cewa tabbas aiyukan soji suna ci gaba da gudana da karfi sosai.

Sanarwar ta kara da cewa " hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuka ba za su taba dakatawa ba, kuma har yanzu na'urorin soji na ci gaba da aiki da karfinsu".

Ta kara da cewa hare-haren da ake kai wa "makiya masu laifin ta’addanci" suna kara tsananta, inda ta yi gargadin cewa yakin na ci gaba da gwabzawa, kuma makiya yahudawan sahyoniya za su fuskanci sakamakon ayyukansu.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha