Sheikh H. Jalala: "Wayewar Addinin Musulunci Itace Hanya Kadai Ta Kiyaye Mutuncin Dan Adam"

Taron Karawa Juna Sani A Jami'atul Mustafa Tanzaniya + Hotuna
16 Oktoba 2025 - 22:55
Source: ABNA24
Sheikh H. Jalala: "Wayewar Addinin Musulunci Itace Hanya Kadai Ta Kiyaye Mutuncin Dan Adam"

Sheikh Hamed Jalala a cikin jawabin nasa, ya bukaci al’ummar musulmin duniya musamman matasa da malamai da su yi zurfafa tunani a kan “Wayewar Musulunci” tare da amfani da ita a matsayin ma’auni domin samun ci gaba mai dorewa. Ya jaddada cewa wannan wayewa ta samar da cikakkiyar mafita ga kalubale na zamani – da suka hada da dabi'u, siyasa, tattalin arziki zuwa jin dadin jama'a.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Babban Shehin Malamin Shi'a Ithnaa Shari'a ta Tanzaniya (TIC), Maulana Sheikh Hemed Jalala Mwakingende, ya halarci wani taron karawa juna sani na musamman na ilimi wanda ya mayar da hankali kan maudu'in "Tushen wayewar Yammacin Turai wajen yin mulkin mallaka a mahangar Sayyid Ali Khamna’i (H.A)".

An gudanar da zaman ne a yau (Alhamis) 16 ga Oktoba, 2025  a Jami’atul-Mustafa (s) da ke bakin tekun Mbezi, Dar es Salaam - Tanzania, karkashin kulawa da jagorancin Hujjatul Islam, Dr. Ali Taqawi, da kuma ta bangaren Academic Research Coordination Unit na Jamiat Al-Mustafa (s), karkashin jagorancin Samahat Sheikh Dr.Reihan Yasin.

A zaman taron Maulana Sheikh Hemed Jalala ya gabatar da cikakken nazari kan maudu’in mai taken: “Tsarin wayewar Yammacin Turai da yadda ake fahimtarsa”.

A cikin jawabinsa, Sheikh Jalala ya bayyana tarihin haihuwar wayewar yammacin turai, da tushenta na ilimi, da kuma yadda ta zama makami na ciyar da manufofin mulkin mallaka da na daidaikun mutane a bangarori daban-daban na rayuwar dan Adam.

Ya yi nuni da cewa, wayewar kasashen yamma ta ginu ne a kan ginshikin son abin duniya, son kai, da mulkin karfi, zalunci, wanda ya sha bamban da wayewar Musulunci da Annabinmu Muhammad (SAW) ya zo da ita, wadda ta ginu a kan ladubba, adalci, daidaito, mutuntaka, da hidima ga dan Adam bisa tushen Tauhidi.

Sheikh Jalala ya kuma bayyana muhimmancin fahimtar wadannan bambance-bambancen ta yadda musulmi za su bunkasa wayewarsu ta musamman bisa tushen Alkur'ani mai girma da Sunnar Manzon Allah (SAW).

Taron ya samu halartar daliban manyan makarantun addinin musulunci, malamai, da shugabannin cibiyoyin addinin musulunci daban-daban na kasar Tanzania. Mahalarta taron sun amfana matuka da tattaunawa da bincike da aka gabatar, wanda ya bayyana mahangar Sayyid Ali Khamenei (H.A) dangane da haqiqanin wayewar yammacin duniya da tasirinta ga al’ummomin duniya.

Sheikh Hemed Jalala: "Wayewar Musulunci Ita Ce Hanya Daya Tilo Da Za A Kiyaye Mutunci Da Martabar Dan Adam".

Mahalarta da dama sun yaba da irin gudumawar da Sheikh Hamed Jalala ya bayar saboda zurfafa nazarinsa, tare da samar da misalai masu rai, da iya kwatanta wayewar Musulunci da na Turawa ta yadda masu sauraro za su iya fahimta da kuma ilmantarwa.

Misalin Rayuwar Wayewar Musulunci

A jawabinsa, Maulana Sheikh Jalala ya tunatar da mahalarta taron tarihin marigayi Imam Ayatullah Ruhullah Khumaini (M.A), wanda ya shelanta kuma ya tabbatar da wayewar Musulunci a aikace ta hanyar juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979 da ya haifar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ya yi nuni da cewa, ta hanyar kokarin Imam, duniya ta ga al’ummar da ta tsaya tsayin daka wajen kare martaba da mutuncin kowane dan Adam, ba tare da la’akari da addini, ko darika, ko kabila, ko launin fata ba. "Sheikh Jalala ya ce wadannan kyawawan tsare-tsare na Musulunci su ne suka samar da al'ummar da ta fifita adalci, daidaito da mutuntaka, ka'idojin da har yanzu Sayyid Ali Khamene'i (Allah Ya kiyaye shi ga Musulunci da Musulmi) yana ci gaba da bunkasawa cikin hikima da tsayin daka".

Kira Ga Ci Gaban Wayewar Musulunci

Sheikh H. Jalala ya bukaci al’ummar musulmin duniya musamman matasa da malamai da su zurfafa tunani a kan wayewar Musulunci tare da amfani da shi a matsayin ma’auni domin samun ci gaba mai dorewa. Ya jaddada cewa wannan wayewar tana ba da cikakkiyar mafita ga kalubale na zamani – da suka hada da ɗabi'a, siyasa, tattalin arziki domin kaiwa ga jin daɗin rayuwar jama'a.

A cewarsa, "ci gaba da riko da al'adu da wayewar Musulunci na ci gaba da kare martabar Dan Adam da kuma samar da zaman lafiya na hakika a duniya".

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha