10 Satumba 2025 - 20:10
Source: ABNA24
Sheikh Naeem Ga Ƙasashen Larabawa: Ku Tunda Baku Da Ikon Maida Martanin Soji Ga Isra'ila Ko Yaya Ne Ku Taimakawa Gwagwarmaya Mana

Babban shugaban kungiyar Hizbullah a kasar Labanon a bayaninsa na zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW): Abin takaici, a ranar 5 ga Agusta, an cimma yarjejeniya wadda da Amurka amma ba a aiwatar da shi ba, Muna kira da a dawo da hadin kan kasa. Kuma muna jaddada bukatar janyewar Isra'ila daga kudancin Lebanon da kuma sakin fursunoni.

Babban shugaban kungiyar Hizbullah ya yi magana ga kasashen Larabawa da cewa: Ku da baku da ikon maida martanin soji ga Isra'ila Alal akallah ku goyon bayan gwagwarmaya mana.

Idan gwagwarmaya ta durkushe, Isra'ila wajenku zata yo. don haka goyon bayan gwagwarmaya na nufin goyon bayan gwamnatin ku da kasar ku. Kada ku soki gwagwarmaya a baya ta hanyar tsayawarku tare da Isra'ila kuma kada ku yi kokarin kwance damarar gwagwarmayar Palasdinawa da kuma yarda da sharuddan sahyoniyawa.

Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ya cikin shirinta na aiwatar da shirin “Babbar Isra’ila”, watakila wata rana za mu ji an kai wa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa hari. Amurka na son kwance damarar gwagwarmaya da kuma mayar da kasar Lebanon ta zama miya mai man shanu ga Isra'ila; idan har hakan ta faru, yahudawan sahyoniyawa za su zo Lebanon don aiwatar da shirin Babbar Isra'ila.

Your Comment

You are replying to: .
captcha