Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: a ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar agaji ta Gaza ta sanar da cewa, sama da gine-gine 50 ne suka rushe gaba daya a hare-haren da Isra’ilan ta kai, kana wasu gine-gine kusan 100 sun lalace, wadanda suka hada da hasumiyai da manyan gine-gine, makarantu, kulab din wasanni da masallatai.
Jami'an kiwon lafiya a zirin Gaza kuma sun ba da rahoton shahadar akalla mutane 21 tun da safiyar yau, ciki har mutane 14 a birnin Gaza.
Sannan Sojoji sun yi wa kauyuka hudu kawanya a arewa maso yammacin birnin Kudus
Your Comment