10 Satumba 2025 - 23:53
Source: ABNA24
Tanzaniya: 'Yan Shi'a Sun Shirya Maulidin Annabi Muhammad (Saw) + Hotuna

Taken Taron Shine: "Manzon Zaman Lafiya” - Dole Ne Zabe Ya Kasance Na Adalci, Dimokuradiyya, Da Zaman Lafiya"

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar mabiya mazhabar Shi'a a kasar Tanzaniya sun gudanar da maulidi na musamman domin murnar zagayowar ranar haifuwar Annabin Allah, Annabi Muhammad Mustafa (a.s) a gundumar Kigogo, a birnin Darus Salaam.

An gudanar da shagulgulan cikin yanayi na aminci da hadin kai da soyayya ga Manzon Allah SAW, tare da rakiyar muzahara da wakokin yabo da addu'o'i da wa'azi daban-daban da ke nuni da kyawawan dabi'un Manzon Allah (saw).

Taken taron:

"Manzon Zaman Lafiya” - Dole Ne Zabe Ya Kasance Na Adalci, Dimokuradiyya, Da Zaman Lafiya".

Wannan maudu’i na da nufin danganta koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da yanayin zamantakewa da siyasa da a aikace, yana mai jaddada muhimmancin adalci, daidaito da kuma hadin kan kasa a wannan muhimmin lokaci na zabe.

An gudanar da wannan biki ne da sakon hadin kai, inda aka yi amfani da taken "littafi daya, Annabi daya, al'umma daya" domin karfafa hadin kai a tsakanin dukkanin musulmi da karfafa komawa ga kur'ani mai tsarki, da tarihinsa, da hadin kan al'ummar musulmi.

A yayin gudanar da muzaharar, masu gudanarwar sun dauki tutocin aminci, suna tunawa da kyawawan dabi'un Manzon Allah (SAW), tare da yin kira ga daukacin al'umma da su tabbatar an gudanar da babban zabe mai zuwa bisa adalci, zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A karshe mabiya Shi'ar Isna Ashariyya na kasar Tanzaniya sun tabbatar da ci gaba da hada kai da kungiyoyin addini da na zamantakewa daban-daban domin isar da sakon Annabi Muhammad (SAW) da kuma ba da gudummawa wajen gina al'umma bisa hadin kai da kima da ci gaba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha