8 Satumba 2025 - 14:52
Source: ABNA24
Jagora: Dole Ne A Yanke Alakar Tattalin Arziki Da Siyasa Ga Isra’ila

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa, ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Sin a baya-bayan nan ta samar da ginshiki na samar da manyan ci gaban siyasa da tattalin arziki wadanda dole ne a bibiye su. Ya kuma yi kira da a dauki kwararan matakai don inganta rayuwar jama’a ba tare da samuwar jiran canji daga waje ba. Jagoran ya kuma jaddada cewa dole ne kasashen musulmi da wadanda ba na Musulunci ba su yanke huldar kasuwanci da siyasa da azzalumar gwamnatin sahyoniyawan, inda ya bayyana ta a matsayin gwamnati wacce aka fi tsana da kyama a duniya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khamenei ya tarbi shugaban kasar da ma'aikatan gwamnati a yammacin yau Lahadi 7 ga watan Satumban 2025. Jagoran ya yi ishara da dimbin laifuka da munanan musibu da yahudawan sahyoniya la'anannu suka aikata, yana mai jaddada cewa: "Duk da cewa irin wadannan laifuffukan suna gudana ne da goyon bayan Amurka amma hanyar da za’a bi wajen fuskanta hakan ba’a toshe ta ke ba, kuma dole ne kasashen da ke adawa da wannan yanayi, musamman kasashen musulmi, su yanke huldar kasuwanci da ma ta siyasa da sahyoniyawa yan mamaya, su kuma yi kokarin mayar da ita saniyar ware".

Jagoran ya bayyana yahudawan sahyoniyawan a matsayin “mafi saniyar ware kuma mafi kyama a duniya,” ya kara da cewa: “kuma dole ne ya zama daya daga cikin manyan hanyoyin diflomasiyyarmu dole mu zaburantar da gwamnatoci da su yanke huldar kasuwanci da siyasa da wannan gwamnati mai aikata laifuka.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mika godiyarsa ga shugaban kasa, jami'ai, manajoji da ma'aikatan gwamnati, musamman ma hukumomin da suka yi kyakkyawan aiki da sadaukarwa na hakika a lokacin yakin kwanaki goma sha biyu. Ya kuma yabawa kwazon shugaban kasar wajen jajircewarsa, da gajiyawarsa, ya kara da cewa, "ziyarar da shugaban da ya yi a kasar Sin ta samu nasara, ta kafa ginshikin samun manyan ci gaba, a fannin tattalin arziki da siyasa, kuma an cimma nasarorin da ya kamata a bibiye su a aikace".

Imam Khamenei ya yi la'akari da "daukar matakan da suka dace a fagen tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a a matsayin muhimmiya kuma cikakkiyar bukata," yana mai jaddada cewa, "Kada mu jira sauye-sauye daga waje don magance matsalolinmu, ko da yake kowane bangare yana aiwatar da ayyukansa a wannan fanni, amma dole ne mu shawo kan yanayin "Ba yaki, ba zaman lafiya" tsaka-tsaki Kenan wanda makiya ke neman kakabawa Iran, domin wannan yanayin yana da hadari da cutarwa ga kasa.

Jagoran ya yi nuni da cewa, “karfafa ginshikin ikon kasa da kuma daukakar kasa, daya ne daga cikin ayyukan gwamnatoci,” ya kara da cewa, “Mafi muhimmanci daga cikin wadannan ginshikan shi ne kyawawan dabi’u, kwadaitarwa, hadin kai, da sanya fata ga al’umma. Wajibi ne a kafasu da karfafasu a maganance da aikace, sannan a dakile hanyoyin raunanasu.

Imam Khamenei ya tabbatar da cewa, "Tabbatar Da Manufofin Musulunci, Koyarwa, Da Dokokin Musulunci, Shi Ne Tushen Samar Da Tsarin Gwamnatin Musulunci", ya ce: "Imam Khumaini (Allah ya jikan shi da rahama) ya shimfida wadannan ginshikan tun daga rana ta farko, kuma duk wanda ya ce akasin haka to ya saba wa maganarsa".

Jagoran ya bayyana jin dadinsa da “yiwuwar samar da daidaito a kasar,” ya kara da cewa, “Hadin gwiwa, hadin kai, da yin aiki tare a tsakanin shugabannin bangarorin gwamnati guda uku abin yabawa ne, amma hukumomi da tsarukan da ke da alhakin yanke shawara da tsara shawarwari dole ne su taka rawar gani a wannan aiki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin al'amarin da ya shafi inganta rayuwar jama'a, yana mai cewa: Ku yi aiki a kan samar da abin da ya shafi inganta rayuwa ta yadda mutane za su iya samun kusan nau'o'in kayayyakin yau da kullum guda goma ba tare da damuwa da tashin farashin kayayyaki ba.

Jagoran ya yi nuni da cewa, abubuwan da suka haifar da raguwar samar da mai, kamar tsofaffin hanyoyi da kayan aiki, ya kara da cewa, "Amfanuwa da kwararrun matasan da suka kammala karatunsu wajen magance matsalolin da kawo sauyi a harkar hako mai da tace shi. Ya kamata kuma a kara zage damtse wajen fitar da mai, sannan a fadada da'irar abokan cinikayya bambanta".

A farkon wannan taron, shugaban kasar Dr. Masoud Pezeshkian ya gabatar da rahoto kan muhimman shirye-shirye da ayyukan gwamnati a cikin shekarar da ta gabata, inda ya bayyana muhimman yarjejeniyoyin da kuma tattaunawa tsakanin Jamhuriyar Musulunci da Rasha, Sin, Iraki, Turkiya, da kasashen Eurasia, inda ya kara da cewa, bangarorin biyu sun kuduri aniyar aiwatar da abin da aka rubuta a takarda.

Dr. Pezeshkian ya ishara da cewa "gwamnati ta ba da kulawa ta musamman wajen bunkasa muhimman ababen more rayuwa ta hanyar kammala manyan tituna, tashoshin jiragen ruwa, da manyan tituna na gaggawa," ya kuma jaddada cewa, "Za a kammala aikin layin dogo na Zahedan-Chabahar kafin karshen shekara." Ya kuma bayyana cewa, “Daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a yakin na baya-bayan nan shi ne yadda direbobin manyan motoci ke jigilar kayayyaki daga tashoshin jiragen ruwa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha