8 Satumba 2025 - 11:45
Source: ABNA24
Yahudawa 5 A Kashe Da Jikkata 16 A Arewacin Birnin Kudus

Kimanin yahudawan sahyuniya 20 ne suka jikkata sakamakon wani harbi da aka yi a mahadar Ramat da ke kan titin Yigal Yadin a birnin Kudus.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: A cewar kafofin yada labaran Ibraniyawa, mutane 6 na cikin mawuyacin hali.

Kamar yadda Majiyoyin labarai suka ba da rahoton wannan farmakin da ‘yan gwagwarmaya suka kai kan yahudawan sahyoniya a mahadar Ramot da ke birnin Kudus da ke mamaya tare da sanar da cewa an kashe yahudawan sahyoniya 5 tare da jikkata wasu 16 a harin.

Kafofin yada labaran yahudawan sun rawaito cewa akalla yahudawan sahyoniya 20 ne suka samu raunuka, 6 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali. Rahotannin farko da kafafen yada labaran Isra'ila suka fitar na nuni da cewa an kashe mutane 5 a harin.

Kafofin yada labaran sun kuma bayar da rahoton shahadar biyu daga cikin wadanda suka aiwatar da aikin farmakar sahyoniyawa.

Kafofin yada labaran yahudawan sun rawaito cewa sojoji da kungiyar Shin Bet suna aiki tare domin zakulo wadanda su kai harbin biyu a babban birnin Falasdinu da aka mamaye. Bayan yunkurin na ‘yan gwagwarmaya gwamnatin yahudawan sahyoniya ta rufe hanyoyin shiga birnin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha