5 Agusta 2025 - 13:44
Source: ABNA24
Al'ummar Kasar Lebanon Sun Fito Kan Tituna Domin Nuna Goyon Bayansu Ga Kungiyar Hizbullah Da Gwagwarmaya + Bidiyo

Batun kwance damara na kungiyar Hizbullah ya sake tasowa a cikin tattaunawar siyasa da shawarwarin diflomasiyya na kasar Labanon, al'ummar Lebanon dai na daukar wannan shiri a matsayin makirci na yahudawan sahyoniya.

Kamfanin dillancin labaran Ahlulbayt na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: a matsayin martani ga karuwar matsin lamba daga kasashen waje da na cikin gida na kwance damarar kungiyar Hizbullah, al'ummar kasar Labanon sun fito kan titunan birnin Beirut domin nuna goyon bayansu ga wannan yunkurin gwagwarmaya na Hizbullah da kuma kin amincewar da faruwar hakan.

A daren jiya ne masu zanga-zangar kasar Lebanon suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga matsayin kungiyar Hizbullah a matsayin daya daga cikin masu fafutukar kare kasar Lebanon.

Masu zanga-zangar dai rike da tutoci da hotunan shugabannin kungiyar Hizbullah, sun yi ta rera taken kare: (gwagwarmaya na da haƙƙin tsayawa gaba da gaba wajen fuskantar masu ketara iyaka na kasashen haure).

Batun kwance damara na kungiyar Hizbullah ya sake tasowa a cikin tattaunawar siyasa da shawarwarin diflomasiyya na kasar Labanon, al'ummar Lebanon dai na daukar wannan shiri a matsayin makirci na yahudawan sahyoniya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha