Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA - ya habarta cewa: A cewar bayanan da aka samu daga harba tauraron dan adam na Nahid 2, an yi nasarar harba tauraron dan adam a sararin samaniya mai tsayin kusan kilomita 500. A cikin wannan faifan bidiyo za mu ga irin nasarorin da aka samu a Iran wajen harba tauraron dan adam Nahid 2.
Taurran Dan Adam nau’in "Nahid 2" ya samu nasarar kafuwa a cikin tazarar kilomita 500 sama da Duniya ga kewayawar geosynchronous
An kera tauraron dan adam (Nahid 2) domin sadarwa bisa kokarin masu bincike daga masana'antar sararin samaniya ta Iran a hukumar kula da sararin samaniya da cibiyar binciken sararin samaniya ta ma'aikatar sadarwa da fasahar Iran, tare da goyon baya da hadin gwiwar wata cibiyar sadarwa ta kamfanoni masu ilimi a kasar.
Kewara da harba wannan tauraron dan adam mai nauyin kilogiram 110 na daya daga cikin muhimman matakai na masana'antar sararin samaniyar Iran wajen sadarwar tauraron dan adam, samar da tsarin tauraron dan adam mai tsayin kasa (LEO) da tsayin sama (GEO).
A cewar Hukumar Kula da Sararin Samaniya, an harba wannan tauraron dan adam da safiyar yau daga sansanin Vostochny na kasar Rasha, kuma an yi nasarar kafa shi a cikin sararin samaniya mai tsayin kusan kilomita 500.
Tare da kewayawar wannan tauraron dan adam, za a gwada fasahar sararin samaniya ta hanyar sadarwar ga Ku-band ta hanyar gwaji a karon farko. Hakanan kuma Sauran fasahohin sararin samaniya irin su kula da halayen axis uku, sadarwa ta hanyoyi biyu a cikin sauran madafan mitar sarrafa bayanai, rarraba karfi, da sauransu kuma za a gwada su a cikin wannan tauraron dan adam.
Tauraron Dan Adam Nahid Zai Yi Aiki Ne Na Tsawon Shekaru Biyu Ne Kawai
Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Iran ya ce: An harba tauraron dan adam Nahid 2 a sararin samaniya a yau - 25 ga watan Yuli - na tsawon shekaru biyu.
A safiyar Juma'a ne na’urar dauka da harba tauraron Dan Adam mai suna (Soyuz) ta harba tauraron dan adam na sadarwa na mai sunan "Nahid 2" daga sansanin Vostochny na kasar Rasha; Hassan Salarieh ya bayyana hakan ne inda ya ce: Bayan da aka yi cikakken kimanta ingancin tsarin na'ura da kerawarsa, tauraron dan adam Nahid 2 ya samu cikakken ingancinsa har ta kaiga ya samu tabbatar ingancin aikin na'urorinsa.
Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Iran ya bayyana cewa: A bisa ka'ida, tsawon rayuwar taurarin dan adam a matakin kasa (LEO) yana da shekaru 5 kuma a tsayin matakin sama na (GEO) yana da shekaru 10.
Dangane da harba wannan tauraron dan adam zuwa sararin samaniya, Salarieh ya kuma ce: Na'urar harba na'urar harba tauraron dan adam na kasar Rasha na daya daga cikin na'urorin harba tauraron dan adam da aka fi amfani da su a duniya, kuma kasashe da dama na sanya tauraron dan adam a sararin samaniya ta wannan na'urar.
Ya yi ishara: A watan Maris na shekarar da ta gabata, aka sanya hannu kan kwangila tare da na'urar harba tauraron dan adam na Rasha don harba wannan tauraron dan adam.
...................................
Your Comment