Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul Baiti (A.S.) - ABNA - ya habarta cewa: Marubucin wannan batun ya bayar da hujjar cewa, bayan yakin kwanaki 12 da Isra'ila, Tehran na neman karfafa karfin soji da goyon bayanta daga kasashen Rasha da China.
Masharhancin na Newsweek ya kuma yi ishara da ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi a makon da ya gabata na halartar taron kolin tsaro na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), inda ya yi kira da a nuna adawa da matakin soja na Washington, da kara yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a ganawar da ya yi da jami'an Rasha da China.
Mujallar ta kammala da cewa, Iran da Rasha sun kara huldar da ke tsakaninsu a farkon wannan shekarar a karkashin yarjejeniyar tsaro da ta hada da atisayen hadin gwiwa, da musayar fasahohin zamani, da kuma hada kai kan barazanar da ake fuskanta.
Your Comment