18 Yuni 2025 - 05:05
Source: ABNA24
Iran Tayi Ruwan Makamai Kan Yankuna A Isra'ila A Harin Ta Karo Na 10

Kafofin yada labaran yahudawan sun sanar da cewa, tun tsakiyar dare Iran ta fara wani sabon zazzafar hare-hare masu karfin gaske daga sojojin kasar mintuna da suka gabata ta hanyar harba makamai masu linzami.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Sojojin Iran ta hanyar fara kai ruɓanyen hare-hare a yankunan da aka mamaye, an yi ta jin kararrawar a duk fadin kasar Falasdinu da ta mamaye.

Harin Iran karo na goma shi ne martani mafi karfi da sojojin Iran suka yi wa yankunan da aka mamaye zuwa yanzu.

An harba makaman ne daga sassa daban-daban na kasar sannan kuma makaman masu linzamin sun nufi yankunan da aka mamaye.

Makamai Masu Linzamin na Iran Sun Kai Hari Kaitsaye Kan Ginin Ma'aikatar Leken Asirin Isra'ila

Duk da hana ɗaukar hotuna da bidiyo daga hukumar yahudawan sahyoniya dangane na irin barnar da hare-haren na Iran suka yi, an fitar da wani faifan bidiyo na wani makami mai linzami da Iran ta kai kan ginin hukumar leken asiri ta sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayyana cewa, 'yan mintoci da suka gabata, yayin da aka fara kai hare-hare da makamai masu linzami da sojojin Iran suka yi a yankuna daban-daban a cikin yankunan da aka mamaye, an yi ta jin karar kararrawa a duk fadin kasar Isra'ila tare da garzayawar jama'a zuwa matsuguni. Kafofin yada labaran Isra'ila sun sanar da cewa makamai masu linzami na Iran sun zama abin tsoro ga mazauna yankunan da aka mamaye. Ƙarfi, tsoro, da damuwa da suke haifar da ci gaban razani na waɗannan makamai masu linzami, wanda kariyar tsaron ƙarfe mai ruɓenyen tsaro na Ƙarfe ba ta iya kare su ba, sun haifar da mummunan tabarbarewar ruhiyya ga dukkan Isra'ila.

An Harba Wani Sabon Makami Mai Linzami A Harin Da Iran Ta Kai Yau A Kan Isra'ila

Yahudawan sahyoniyawan ba su lura da shi ba sai bayan da ya sauka. Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Iran: An yi amfani da wani sabon makami mai linzami a harin da sojojin kasar suka kai a yau a kan gwamnatin sahyoniyawa, wanda yahudawan sahyuniya suka sanar da cewa ba su lura da shi ba kafin a saukarsa.

Kwamandan Rundunar Sojin Kasar Iran: An fara kai hare-hare da makamai masu linzami da sabbi da na zamani kuma za su kara tsananta nan da sa'o'i masu zuwa.

Makami Mai Linzamin Iran Ya Kai Hari Kan Ginin Leken Asirin Sojojin Isra'ila (Aman)

Kafofin yada labaran Isra'ila sun kuma sanar da cewa sama da makamai masu linzami 20 ne suka fada a yankuna daban-daban na yankunan da ta mamaye.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a yayin wani harin makami mai linzami da Iran ta kai kan birnin Petah Tikva, wani makami mai linzami kai tsaye ya afka cikin wata mafaka, inda ya kashe sahayoniya hudu. Harin makami mai linzami da Iran ta kai kan Isra'ila tare da kashe sahayoniya da dama a wani matsuguni ya haifar da fushin jama'a a tsakanin al'ummar yankunan da ta mamaye.

Rashin amincewar da yahudawan sahyuniya suka yi da kayayyakin kariya na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya mayar da sararin yanar gizo wani fagen nuna adawa da fushi.

Wani makami mai linzami na Iran ya afkawa wani gini kai tsaye a yankin Herzliya dake arewacin Tel Aviv. Ana iya ganin ginshikin hayaki a Herzliya bayan harin makami mai linzami na Iran.

Bayan wani sabon harin da Iran ta kai kan yankunan da aka mamaye, tashar 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, ana iya jin karar fashewar wasu abubuwa daga Ramat Hasharon da ke kusa da birnin Tel Aviv.

Hotunan da aka fitar daga garuruwan Tel Aviv, Herzliya, Ramat Hasharon da wasu yankuna da dama na nuni da cewa kusan makamai masu linzami 20 ne suka afkawa wurare daban-daban, inda suka yi barna da hasarar rayuka. Duk da cewa sama da sa'a guda kenan da harba makamin na Iran, har yanzu hayaki na tashi daga daya daga cikin gine-ginen da ke Tel Aviv.

Your Comment

You are replying to: .
captcha