Gaza
-
Amurka Ta Ɗauki Alhakin Gudanar Da Kamfanonin Siminti A Kan Iyakar Gaza
Rediyon sojojin Isra’ila ya ba da rahoton cewa an bawa Amurka hakkin kulawa da samar da kuɗaɗe da gudanar da kamfanonin siminti a kan iyakar Gaza; kamfanonin da aka kafa don samar da kayan da ake amfani da su wajen rufe ramummuka. A lokaci guda, wannan kafar ta yi iƙirarin cewa Benjamin Netanyahu da "Yisrael Katz" sun amince a asirce da fara wani aiki don ƙirƙirar ababen more rayuwa da gina rukunin gidaje na Falasdinawa a gabashin Rafah; iƙirarin da ofishin Netanyahu ya bayyana a matsayin karkatarwa ga abinda yak e faruwa a gaske da yada bayanan da suka shude a baya.
-
Rahoto Cikin Hotuna |Yadda Mazaunan Gaza Suke Fuskantar Matsalolin Ruwa
Babban daraktan Hukumar Ruwa ta Gaza ya yi gargadi game da tabarbarewar rashin ruwa a Zirin, inda ya bayyana cewa bayan barnar da aka yi wa manyan cibiyoyin ruwa, yawancin hanyoyin ruwa da magudanar ruwa sun lalace, kuma mazaunan Gaza suna fama da mummunar taɓarbarwar rashin ruwa da kamuwa da ƙishirwa.
-
Kaitsaye Cikin BIdyiyo
Yadda Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Wurin Aikin Ƙarfe A Titin Masana'antu A Birnin Gaza Mintuna Kadan
Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA - Lokacin kai hare-hare a wurin aikin ƙarfe a titin masana'antu a birnin Gaza kadan da ya wuce.
-
Gaza: Shahidai 5 Da Jikkatar 7 Sakamakon Hare-Haren Isra’ila A Gaza A Cikin Sa'o'i 24
Ma'aikatar Lafiya ta zirin Gaza ta sanar da samun shahidai 5 da raunata 7 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a ci gaba da asarar rayuka sakamakon ta'addancin Isra'ila.
-
Shahadar Jariri A Yammacin Ramallah Bayan Mamaya Ya Hana Kai Shi Asibiti
Majiyoyin lafiya a yau Lahadi, sun tabbatar shahadar wani jariri sakamakon hanawar da sojojin mamaya don kai shi jinya ta ƙofar Deir Ammar da ke yammacin birnin Ramallah wadda aka rufe tun watanni 5 da suka gabata.