Jagora ya fara da taya su murnar kammala wannan marhalar ta jarabawa, wanda yace a wancan karon da kotu ta wanke mutum 24 daga cikinsu, ya bayyana taya su murna, inda yace ba cikakkiyar murna ba ce a lokacin, saboda rashin fitowan ragowar.
Shaikh Zakzaky ya bayyana hukuncin da alkalin kotun da ta musu shari’a ya yi a matsayin abin mamaki, saboda cewarsa ya samu ‘yan uwa da laifi. Yace: “Mu abinda muka tsammata, in ma har zai ce ya samu wasu da laifi, zai ce ya same su da laifi ne, amma hukuncin da za a yi musu kan laifuffukan, to an tsare su fiye ma da ninkin baninkin horon da za a yi musu, saboda haka da zai ce ne ma su tafi kawai. Amma sai ya zo da wani karin abinda ke da ban al’ajabi, shi ne wai a ci tara. Taran kuma har da ma biyan kudin wata mota da aka kona".
Yace: “Wannan ya zama wani abu da ya zama na farko tun lokacin da muke Harkar nan, tun saba’inoni, tun kila a lokacin shi wannan jojin yana Firamare. Tun a lokacin ba a taba kai mu kotu aka same mu da laifi ba, ko sau daya. Sukan dai kai mu, amma karshe sukan ce ba a yi laifi ba. Amma shi wannan sai yace ya samu laifi".
Ya kara da cewa: “An sha kai mu kotu, amma ba a samunmu da laifi, kuma wani bai taba cewa an same mu da laifin ‘unlawful assembly’ ba, saboda ba doka ba ne, amma wannan shi ya samu. Amma ya fadi wasu abubuwa guda biyu muhimmai; yace ba laifi ne a zama Shi’a ba, kuma ba laifi ne ya zama ana Islamic movement ko? Jayyid! Wannan ‘is good’ ”.
Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda ‘yan sanda kan kama ‘yan uwa a lokuta daban-daban bisa laifin cewa su Shi’a ne. Yace: “Ko da yake daga baya sun zo sun ce ba laifi ba ne a yi Shi’a ba, wai suna fada da IMN ne. To sai kuma gashi shi wannan Jojin yace ba laifi ne a yi IMN ba, wanda dama su suka kirkiri sunan suka ce akwai”.
Jagora ya jaddada cewa mu ba kungiya ba ce. “Mu ba kungiya ba ne, bamu taba tunanin kanmu a matsayin kungiya ba. Mu mun ce mu addini muke yi, kuma bamu taba sanin inda za a ma addini rigista ba”.
Yace, hukuncin da da alkali Belgore ya yanke na cewa ‘yan uwa sun yi laifi da suka yi taro ba tare da sun nemi izinin ‘yan sanda ba, yana nufin kenan duk wani taro ko da na sallar Juma’a, da Jana’iza, da daurin aure, da taron radin suna, da masu wasa da maciji akan hanya, da masu sai da maganin gargajiya a hanya, da makamantansu duk sai an rika neman izinin ‘yan sanda kafin a yi su, tunda su ma ana tara mutane ne a waje guda.
“Mu kaddara ma akwai wata doka da ta hana yin taro, to tambaya; wanda ya kira taron ne ya yi laifi, ko wanda ya je taron? Saboda alal misali, idan kana bukatar sai an baka izinin ka kira taro, sai wani ya je ya nemi izini aka bashi, sai ya kira mutane suka zo, to duk wanda za su zo taron nan sai sun je sun karbi izini, ko kuwa shi da ya kira taron ne yake neman izinin?” Jagora ya tambaya.
Yace: “In ma akwai abinda ake kira ‘legal assembly’, wanda sai mutum ya nemi izini an bashi, to wanda ya kira taron ne yake bukatar ya yi, ba wanda aka gayyata ba. Saboda haka in ma aka taru ba izini, wanda ya kira taron ne ya yi laifi, ba wanda ya je ba. In kuwa har ma wanda suka je ma sun yi laifi, (kuma za a kama su da laifi ne) to kamar yadda nake cewa lokacin da ‘yan mulkin mallaka suke yi a nan, suna da ka’idar sai an saka abin magana kowa ya ji, cewa taron nan da kuke yi ya saba doka, saboda haka muna umurtanku ku watse, in baku watse ba za mu kama ku mu kai ku kotu. In kuma aka kama ku aka kai ku kotu, to taron Fam daya ne, ki daurin wata shida, saboda kun saba ma sarauniya”.
Shaikh Zakzaky ya bayyana Alkali Belgore a matsayin wanda ya saba doka da yin wannan hukuncin ga ‘yan uwa. Yace: “Ya yi abinda ya yi, amma shi kansa ya saba doka. Kuma lallai za mu je kotu na gaba. Don ba za a kyale wannan tabargaza ya cigaba ba. Ba a taba tabargaza irin wannan ba, tun 1970s ban taba jin an daure mutum akan wannan ba, tunda muke Harkar nan, ba a taba ce mana wai wani ya yi taro ba izini ba, sam! Don bashi a doka. Amma shi yanzu yace ya samu mutane da laifin da bashi ma a doka”.
Yace: “Shi kuwa ‘mischief with fire’ (da yace ‘yan uwa sun yi), to babban ‘mischief’ shi ne wannan wanda ya yanke hukunci din. Ba yadda za a yi ka samu mutum 33 kace sun kona mota daya. In ma an kona mota sai a samu wa ya kona ko? Amma kace mutum 33 duk cikarsu sun kona mota, zai yiwu?”.
Ya kuma tambaya akan shin su ‘yan sanda basu yi laifin komai ba? Yace: “Tunda yace an wanke duk wanda aka kawo kotun daga laifin kashe dan sanda da dan jarida, to tambaya, wa ya kashe dan sanda, wa kuma ya kashe dan jaridan? Ko shikenan, don ba a samu ‘yan uwa da laifi ba, shikenan ba wanda ya yi laifin kenan? Kisan dan sandan nan ba laifi ba ne? Dole akwai wanda ya yi ko?”.
“Tunda dai kisan da aka yi laifi ne, to dole a samo dan sanda da ya kashe dan sandan, kuma dole a samo dan sandan da ya kashe dan jarida din, ko kuma a dora ma ‘yan sandan alhakin cewa sun yi harbe-harbe ba bisa ka’ida ba!” Inji Shaikh Zakzaky.
Ya bayyana wa Alkali Belgore cewa, ya yi kuskure, kuma ya bata sunansa da ‘record’ din aikinsa, kuma abinda ya yi zai bi shi kamar yadda zai bi wadanda suka afkawa ‘yan uwa da kisa da barna, suka kawo masa ya yanke hukuncin zalunci.
Da ya juya ga ‘yan uwan da aka sake, Jagora ya jinjina musu tare da tabbatar musu da cewa hakarsu ta cimma ruwa, kuma azzalumai ne suka ji kunya. Yace: “A lokacin da suka tsare mu, mun kai su kara mun yi nasara, sun kai mu, mun yi nasara, saboda haka ta yaya to wanda aka ce a sake mu, zai zama shi kuma an same shi da laifi? Kaga da abin mamaki ko? Wanda ya fito yana cewa a sake mu, sai a same shi da laifi? Tsarewa (ne aka mana) da ya saba ma ka’ida, ashe wanda duk yace a sake mu ya yi daidai”.
Yace: “Mun san cewa dama akwai jarabawa. Hanyar haka ta gada. Dama laifin wanda yace yana bin tafarkin Allah, laifinsa shi ne bin tafarkin Allah din. In dai ka tsaya kyam baka yi biyayya gare (azzalumai) ba, kace Ubangijin da ya halicceka za ka bi, to ka yi musu laifi, ta kowane hali kuma sai sun same ka da wannan laifin. Ta kowane hali, shi ma’abocin addini ya yi laifi ne. Kuma wannan laifin Annabawa duk shi suka yi. Ba Annabin da bai yi wannan laifin ba”.
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa, babu wani Annabi da ya zo ga al’ummarsa suka karbe shi hannu bibbiyu, face sun yi yunkurin kashe shi ma. “Ba wata al’ummar da ta yi ma Annabinta maraba. Bihasali ma ba wata al’ummar da bata yi aniyar kashe Annabinta ba. Meye laifinsa? Sakon da ya zo da shi. Yace; ba ku da wani Ubangiji in ba Allah ba. Shi kuma yace Ubangijinsa shi ne Allah, wannan ne laifin, domin su in dai za ka yi musu biyayya, kace su ne iyayen giji, to ya yi daidai, kai ne dan kasa na gari mai biyayya (a wajensu)”.
Shaikh Zakzaky yace, rukushi ne ga azzaluman kasar nan yadda suka karairaya dokokin da suka rubuta da hannunsu a kan ‘yan uwa Musulmi. “Ba kawai dokokin Allah suke karyawa ba, har da dokokin da suka rubuta da hannayensu sun karairaya su. Sun karya duk dokan da su da kansu suka rubuta. Don dokarsu ta ba da damar ‘yancin addini, ‘yancin fadan albarkacin baki, ‘yancin haduwa da mutanen da kuke da ra’ayi daya ku bayyana ra’ayinku, gasu nan da dama, duk suka danne wannan”. Ya jaddada.
Yace: “Mu inda muke samun kwanciyar hankali shi ne, mun san cewa jarabawa ce. To kuma jarabawa din nan lazim ne za a jarabaka. Ba za a kyale ka ba don kace ka yi imani. Za a jarabaka. Jarabawar nan kuma marhala marhala ce daban-daban”.
Ya cigaba da cewa: “Jarabawa ce wasu Allah Ta’ala ya karrama su da shahada sun tafi. Allah Ta’ala ya karbi shahadarsu. Wasu kuma an ji musu rauni har an kassara su. Wasu kuma an tursasa, an tsare, abubuwa daban-daban ba wanda ba a yi ba. Wanda a tarihin kasar nan ba a taba sanin wanda aka ma wani abu mai kama da haka nan ba”.
Yace, “Wannan abin da ya same mu kadan ne daga abinda Allah Ya jarabci na farko da shi, ba mu fatan Allah Ya jarrabce mu da abinda aka jarabci na farkon. Kuma kadan ne in an kwatanta da abinda ‘yan uwanmu na Palasdinu ke fuskanta a wannan lokaci namu. Wanda suke fuskantar yunkurin share al’umma gabadayanta, har ya zama kullu-yaumin za ka ji an ce an share gida gabadaya, mai uba, da uwa, da ‘ya’yansu… Kuma suna nan sun dake, suna jiran hukuncin da Allah zai yi; ko dai su tafi, ko kuma Allah Ya rayar da su su yi nasara”.
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa ana sadaukarwa ne saboda addinin Allah, ba domin gina duniya ko samun bukatun duniya ba. Yace, in mutum ya ba da ransa don gina kasa (alal misali), to ina zai rayun da zai amfana da wannan kasar? Amma in saboda Allah ne, ai zai koma wajen Allah ne. “Ta nan ne zai iya dakewa, ko da zai rasa ransa, saboda ya san zai koma wajen Allah din ne. Shi yasa kuma ba yadda za ka kwatanta mai yi don Allah, da mai yi domin wani dalili. Ba za su taba haduwa ba, saboda mai yi don Allah Ya san saboda me yake yi. Abinda ya bambanta mu kenan da sauran, saboda yi don Allah".
A nan ne ya jawo hankalin yan uwan akan yin komai saboda Allah Ta’ala. Yace: “Iklasi muhimmin abu ne. Yanzu an je makaranta na wajen shekara shida a jere, bayan abinda aka hadu da na wahalhalu daban-daban, amma kuma an koyi darussa daban-daban, to yanzu fatanmu shi ne Allah Ta’ala ya kambama lada. Ya ba da ladan wannan marhala da aka yin a jarabawa. Ya kuma amfanar da mu da al’umma gabadaya da wannan marhala ta jarabawa da kuka wuce. Kuma muna fatan Allah Ta’ala ya bamu sabati. Ya sa mu ga natijan wadannan sadaukarwa da aka yi. Ya kwato mana sauran ‘yan uwa da ake tsare da su a wurare daban-daban”.
A karshe, Jagora ya yi addua ga Shahidai da iyalan Shahidai masu girma, da fatan jinanensu da sadaukarwarsu ya yi tasiri wajen rayar da addini.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
01/DhujHijja/1446
29/05/2025
Your Comment