ABNA24 : Bobi Wine da sauran yan takaran da suka shiga zaben sun yi zargin tafka magudi.
A sakamakon zaben, Museveni ya samu kashi 58.64% na kuri'un da aka kada yayin da babban abokin hammayassa Bobi Wine ya samu kashi 34.83%.
Kafin hakan dama Jagoran ‘yan adawan na Uganda ya nuna damuwa akan yadda sojoji suka yiwa gidansa kawanya gabanin fitar da sakamakon zaben.
M Bobi Wine, ya kuma koka kan cin zarafin magoya bayansa da jami’an tsaro suka yi, da kuma hana wa magoya bayansa sayan ido a zaben.
Shugaba Museveni mai shekaru 76 ya shafe shekaru 34 yana mulkin kasar, wanda a yanzu kuma zai mulki kasar na wani wa’adin mulki karo na shida, idan kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da nasararsa a wannan zaben.
342/