ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Al-Wasad na kasar ta Libya ne, ya bada wannan labarin. Ya kuma kara da cewa kwamitin rubuta kundin tsarin mulkin ya bayyana haka ne a taron da ya gudanar ta kafar yanar gizo karkashin kula na ofishin jakadancin MDD da ke kasar. Majiyar MDD a birnin Tripoli ta kara da cewa wannan kwamitin mai mambobi 18 zai sake gudanar da wani taro a cikin mako mai zuwa don tattaunawa kan shawarorin da ya bayar kan yadda za’a gudanar da zabubbukan majalisar dokoki da kuma na shugaban kasa a cikin watan Desamba na wannan shekarar.
342/