ABNA24 : Daga cikin wadanda aka sako din har da tsohon dogarin marigayi shugaba Kabilan wato Kanar Eddy Kapend da kuma tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Georges Leta wadanda a wancan lokacin aka same su da hannu cikin makarkashiyar kasha shugaba Kabilan a shekara ta 2001.
Tun da fari dai an yanke wa mutane 22 da aka sako din ne hukuncin kisa, to sai dai a watan Yunin da ta gabata shugaba Tshisekedin ya mayar musu da hukuncin zuwa ga dauri a gidan yari, kafin daga baya watan Disamban da ta gabatan nan yayi musu afuwa bayan rushewar hadakar da ya kafa da magoya bayan tsohon shugaban kasar da ya gada wato Joseph Kabila.
Mataimakin ministan shari’ar kasar Bernard Takaishe ya ce shugaban kasar ya dau wannan mataki na yin afuwa wa mutanen ne saboda dalilai na jin kai da kuma kokarin gwamnati na sake dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
A ranar 16 ga watan Janairun 2001 ne dai daya daga cikin masu gadin tsohon shugaba Kabilan ya bindige shi har lahira a cikin ofishinsa, inda shi ma nan take bayan ya fito daga ofishin babban dogarin shugaban ya bindige shi har lahira duk kuwa da yana da damar kama shi lamarin da ya sanya daga baya ake zarginsa da hannu cikin kisan gillan da kuma cewa ya kashe mai gadin ne don ya rufe bakinsa kar a gane hannun da yake da shi a ciki, lamarin da tun a lokacin dai ya musanta.
342/