ABNA24 : Mista, Zarif ya wallafa a shafinsa na tiwita, cewa, jinjina ga Qatar akan juriyar data nuna bisa matsin lamba.
A hannu daya kuma ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya mika sako ga makobtan kasarsa da cewa ‘’ Iran ba abokiyar gaba ba ce ko barazana, ga kowa, don haka lokaci ya yi da ya kamata ku karbi tayinmu na zamar da yanki guda mai karfi, saboda wanda ke ingiza ku yana kan tafiya…
A jiya ne dai Saudiyya ta sake bude iyakokinta na sama da kasa dana ruwa da kasar Qatar, bayan shafe sama da shekara uku a garkame biyo bayan tsamin dangantakar diflomatsiyya tsakanin kasashen biyu makobtan juna.
A watan Yuni na shekara 2017, ne Saudiyya da kawayenta Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain, da Masar suka yanke huldar diflomatisyya da Qatar bisa zarginta da goyan bayan kungiyoyin masu tsatsauran ra’ayin islama da kuma kusanci sosai da Iran, batun da Qatar din ta sha musantawa.
342/