ABNA24 : Sakataren ma’aikatar watsa labarun Nick Mangwana ne ya sanar da cewa; “gwamnati tana daukar mutanen na yankin Chimanimani ne zuwa yankuna masu aminci saboda kaucewa barnar da mahaukaciyar guguwar za ta iya haddasawa.”
A halin da ake ciki dai guguwar wacce aka bai wa sunan; Chalane, tana kadawa a cikin kasar Mozambique, za kuma ta iya rikidewa zuwa mahaukaciya tare da ruwan sama mai karfi a cikin kasar baki daya, musamman a yankunan gabashin kasar dake kan iyaka.
Da akwai cibiyoyi 20 da gwamnatin kasar ta samar a cikin gundumar Manicaland.
A shekarar da ta gabata mai dubban mutane ne su ka rasa rayukansu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Idai,a kasar da har yanzu wasu daga cikinsu suna rayuwa a cikin hemomi.
342/