ABNA24 : Zulum ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ziyarci inda wasu mahara suka yi awon gaba da matafiya 35 a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, hanya daya mai lafiya ta rage zuwa jihar Borno.
Da yake ganawa da manema labarai a wurin, Gwamna Zulum ya bayyana matukar bacin ransa dangane da faruwar al’amarin, duk da yadda aka jibge dimbin jami’an tsaro daban-daban a kan hanyar, amma a cewarsa hakan bai magance irin wadannan hare-hare a kan babbar hanyar ba.
“Gaskiya wannan babban abin bakinciki ne dangane da yadda ake ci gaba da awon gaba da matafiya tare da kashe su a wannan hanya ta Maiduguri har zuwa Kano, musamman tsakanin Maiduguri da Damaturu.
Bayan sace daliban sakandare ta Kankara a jihar katsina ne kuma aka sace wasu matafiya 35 a kan hanyar Damaturu Maidugiri, wanda ake sa ran ‘yan ta’adda na Boko Haram ne suke da hannu wajen sace mutanen, wadanda har yanzu ba a san makomarsu ba.
342/