ABNA24 : Dukkan wadandan kwamandojin guda biyu sun yi shahada ne a wani hari da aka kai musu da jirgi mara matuki bisa umurnin shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trumph a kusa da filin saukar jiragen sama na birnin Bagadaza na kasar Iraki a ranar 3 ga watan Janerun shekara da muke ciki, wanda Janar Sulemani ya je ziyarar aiki ne bisa gayyatar da gwamnatin kasar Iraki ta yi masa.
Har ila yau jagoran ya kara da cewa Jana’izar da ka yi musu da ta samu halartar miliyoyin mutane lamari ne da ba za’a taba mantawa da shi ba kuma ya jefa ma’abota girman kai na duniya cikin mamaki , kuma shi ne mari na farko a fuskar Amurka.
Kuma kai hari kan sansanin sojin Amurka a Ainul Asad dake Iraki shi ma wani mari ne a fuskar Amurka , sai dai wannan ya banbanta da martani mai tsananin da zaa’a kai da yake jiran wadanda ke da hannu wajen kashe Kasim Sulemani.
Daga karshe jagoran ya nuna cewa shahadar Kasim Suleman mai cike da tarihi ta mayar da shi wani babban gwarzo ba kwai a kasar Iran ba, hatta a wajen dukkan al’ummar musulmi.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau, inda yake tabbatar da cewa, babu makawa Iran za ta mayar da martani kan kisan Qasem Sulaimani a lokaci da kuma wurin da ta ga ya dace domin yin hakan, kamar yadda kuma martanin zai shafi wandanda suka bayar da umarnin yin hakan, da kuma wadanda suka aiwatar.
Dangane da batun janye takunkumai a kan Iran ya ce bas hi da wata matsala kan hakan, idan gwamnatin kasar ta ga akwai hanya mafi sauki domin aiwatar da hakan, amma bai kamata a amince da yaudarar makiya ba.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, yana yin yin kira ga jami’an gwamnatin kasar, su mayar da hankali ne wajen rusa takunkuman da aka drawa kasar, maimakon mayar da hankali wajen neman janye su.
Jagoran juyin juya halin na Iran ya ya kara da cewa, Amurka ta kashe fiye dad ala biliya bakawai domin rusa kasashen Syria da Iraki, amma burinsu bai cika ba har yanzu, kuma ba zai cika ba.
Dangane da kasashen turai uku da suke cikin yarjejeniyar nukiliya tare da Iran, wato Jamus, Burtaniya da Faransa, ya bayyana su da cewa da cewa kasashe ne masu tsabar munafunci da yaudara.
342/