ABNA24 : Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana a shafinsa na twitter, cewa amfani da takunkumin da Amurke ke yi kan kasashe ya wuce gona da iri.
A jiya ne dai gwmanatin Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan kasar ta Turkiyya, saboda sayan makaman garkuwa samfarin S-400 kirar kasar Rasha.
Ita ma dai a nata bangare kasar ta Rasha, ta yi tir da takunkumin Amurkar kan kasar ta Turkiyya.
342/