ABNA24 : Mai Magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Iran din Sima Sadat Lary, ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu jumillar adadin wadanda cutar ta kashe tun daga bullar ta a Iran, sun kai dubu 50 da 16.
Su kuwa wadanda su ka warke daga cutar bayan kamuwa da ita sun kai dubu 719 da 708, amma kuma abin takaici acikin sa’oi 24 da suka wuce wadanda cutar ta kashe sun kai 321.
Wadanda kuwa aka yi gwajin a wannan tsakanin su ne miliyan 6 da dubu dari 342 da 628.
342/