ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRAN PRESS ya nakalto kakakin hukuma mai kula da abinci da magunguna na kasa yana fadar haka a jiya Laraba. Kianush Jahanpour ya bayyana haka ne a cikin shafinsa na twitter jiya da yamma, ya kuma kara da cewa, wannan wata alama ce ta cewa kasar Iran ta shiga jerin kasashe masu fasahar samar da alluran rigakafin cututtuka a duniya.
Kafin haka dai wakilin hukumar lafiya ta duniya WHO a Tehran Christoph Hamelmann ya bayyana gamsuwarsa da yadda shirin samar da allurar riga kafin cutar ta korona yake tafiya a nan Iran a wani taron da aka gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamban da ya gabata a nan Tehran.
Ya kuma kara da cewa takunkuman tattalin arziki masu tsananin wadanda Amurka ta daurawa kasar basu yi tasiri a ci gaban da kasar take samu na ilmi ba.
342/