ABNA24 : Majiyar MDD ta ci gaba da cewa; Kashe mutane da wannan adadi mai yawa da yakin na kasar Yemen yake yi, wani abu ne wanda ba za a yarda da shi ba.
Don haka MDD ta yi kira da a tsagaita wutar yaki a Yemen din, domin an isa wata gaba da bai kamata a wuce ta ba.
Bayanin da MDD ya zo ne adaidai lokacin da ake juyayin kisan da aka yi wa mata 14 a gundumar al-Hudaidah dake uammancin kasar kwanaki biyu da su ka gabata.
Tun a 2015 ne dai Saudiyya da HDL su ka shelanta yaki akan kasar Yemen, da hakan ya safa jefa kasar cikin matsananciyar wahala.
Baya ga dubun dubatar mutanen da su ka kwanta dama, wasu duban dubatar sun jikkata, kamar kuma yadda wani adadi na mutanen kasar su ka zama ‘yan gudun hijira.
342/