1 Disamba 2020 - 10:42
​OPEC Za Ta Tattauna Yiwuwar Rage Yawan Danyen Man Da Take Fitarwa

A yau ne kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC da mukarrabanta ke fara gudanar da taro ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, domin tattaunawa a kan rage yawan danyen mai da kasashe mambobin kungiyar suke fitarwa.

ABNA24 : Taron na zuwa ne a lokacin da ake zaton cewa bangaren man fetur zai murmure daga mummunan tasirin annobar corona, wadda ta tilasta wa kungiyar OPEC rage yawan danyen man da take samarwa, saboda raguwar bukatar danyen mai a duniya.

Kasashen da ke cikin wannan kungiyar dai na kokarin ganin sun dauki matakan da za su taimaka domin kaucewa faduwar darajar mai, irin wanda aka samu a watannin baya.

Bisa yarjejeniyar da aka cimmawa a watan Afrilun, ana sa ran sake rage ganga miliyan 7 da dubu dari 7 na danyen mai da ake samarwa kowace rana, zuwa miliyan 5 da dubu dari 8 duk rana a watan Janairun 2021.

Wasu na ganin cewa mai yiwuwa samar da allurar rigakafin cutar corona ya yi tasiri wajen kara habbaka darajar danyen mai a kasuwanninsa na duniya, duk da cewa matakin rage yawan mai da kashe mambobi a kungiyar suke fitarwa, shi ne abin da wasu daga cikinsu suke fifitawa, wajen sake daga darajar farashin gangar mai a duniya.

342/