30 Nuwamba 2020 - 12:08
Jam’iyyar Shugaban Kasa A Kasar Burkina Faso Ta Kasa Samun Rinjayen Kujeru A Majalisa

Jam’iyyar shugaban kasar ta Burkina Faso (MPP ) wacce tun bayan kifar da gwamnatin Blaise Compore ta samar da shugabanni kasashe uku, ta kasa samun rinjaye a majalisar dokokin kasar.

ABNA24 : A wata sanarwa da hukumar zaben kasar ta yi, ta ce; Jam’iyyar da yake mulki ta sami kujeru 56 ne a tsakanin kujeru 127 da ake da su a majalisar dokokin kasar. Jam’iyyar tana da bukatuwa da kujeru 64 domin ta zama mai rinjaye.

A zaben shugaban kasar da aka gudanar, jam’iyyar shugaban kasar ta sami kaso 57.87 na jumillar kuri’un da aka kada.

Manazarta harkokin siyasar kasar suna hasashen yiyuwar kulla kawance a tsakanin jam’iyyar mai mulki da kuma jam’iyyar NEW TIMES PARTY, wacce ta sami kujeru 5 kadai majalisar dokokin.

342/