28 Nuwamba 2020 - 12:38
‘Yan Majalisar Dokokin Kasar Iraki Sun Bukaci Gwamnatin Kasar Ta Maida Martani Ga Hadaddiyar Daular Larabawa

Bayan da gwamnatin Hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta dakatar da Visar shiga kasar daga kasashen 13 daga ciki har da kasar Iraki, da kuma kama wasu daga cikin yan kasar Iraki mazauna kasar ,wasu yan majalisar dokokin kasar sun bukaci gwamnatin kasar ta maida martani.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Mukhtar Al-Musawi mamba a kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin kasar ta Iraki ya na cewa dole ne gwamnatin kasar Iraki ta maida martani, wato ta hana yan kasar UAE shiga kasar, sannan ta gudanar da bincike don gano dalilan da suka sa aka kama ‘yan kasar ta Iraki a UAE sannan ta yi kokarin hadasu da iyalansu.

Har’ila yau wani dan majalisar mai suna Hassan Ali ya bukaci gwamnatin kasar ta kira jakadan UAE a Bagdaza don yi masa gargadi.

Majiyar majalisar ta bayyana cewa matakan da gwamnatin UAE take dauka ba zai rasa nasaba da samar da huldar jakadanci da HKI da ta yi ba. Labarin ya kara da cewa, mafi yawan kasashen da ta dau matakin hanasu Visar, wadanda basa dasawa da Isra’ila ne.(19)

342/