23 Nuwamba 2020 - 17:54
​Iran:Mutane 453 Ne Suka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Cutar Korona A Yau Litinin

Kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata, mutane 453 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar Cutar Korona.

ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Mususlunci ta Iran (JMI) ta nakalti Simo Sadat-Lari tana fadar haka a yau da rana, ta kuma kara da cewa jimillar wadanda cutar ta kashe tun bayan bullarta a farkon wannan shekara ya kaia 45,255. Sai kuma sabbin wadanda suka kamu da cutar a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata ya kai mutane 12,460, inda 2,744 suna kwance a asbitocin kasar a yayinda sauran kuma suke jinya a gidajensau.

Har’ila yau Sadar Lari ta kara da cewa matakan da kwamitin yaki da cutar ta dauka na tilastawa mutane zaman gida na makonni biyu ya fara tasiri. Don haka ta bukaci kwamatin ya ci gaba da daukar irin wadannan matakan.

342/