ABNA24 : Yayin da kuma yake magana kan sanarwar da kasashen Turai da suka sanya hannu da Iran kan yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma a shekara ta 2015, jakadan na Iran ya ce biyo bayan yadda Amurka ta yi gaban kanta wajen ficewa daga yarjejeniyar, babu wani abin da wadannan kasashen turai din suka yi face dai nuna damuwarsu kawai da kuma ci gaba da nuna damuwarsu kan yadda Iran ta rage irin yadda take ba da hadin kai da kuma aiwatar da yarjejeniyar wanda Iran din ta ce ta yi hakan ne don mayar wa kura aniyarta sakamakon ficewar da Amurka ta yi daga yarjejeniyar wanda shi a kan kansa hakan karen tsaye ne ga yarjejeniyar, inda ya ce duk da hakan kasashen Turan ba su dau wani mataki na azo a gani ba.
A cikin sanarwar da wadannan kasashen na turai su uku wato Ingila, Faransa da kuma Jamus suka fitar, sun bukaci Iran da ta gaggauta yin watsi da wannan mataki sannan kuma ta gaggauta dawowa da kuma aiwatar da cikakken nauyin da ke wuyanta na yarjejeniyar nukiliyan.
Bayan fitar da wannan sanarwar dai, Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta bakin mai magana da yawunta Saeed Khatibzadeh yayi watsi da wannan matsaya ta Turawan da ya kira da matsayar rashin mafadi na wadannan kasashen turai ukun, yana mai kiransu da su dakatar da wannan zargi na siyasa da suke wa Iran su yi kokari wajen sauke nauyin da ke wuyansu kamar yadda ya zo cikin yarjejeniyar ta nukiliya.
342/