22 Nuwamba 2020 - 13:17
​Kungiyoyin Musulmi Sun Yi Allawadai Da Wa’adin Da Macron Ya Bawa Musulman Kasar Faransa

Kungiyoyin musulmi suna ci gaba da yin allawadai da wa’adin makonnin biyu wanda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bawa musulman kasar na bayyana yadda musulman kasar suke daukar yencin bil’adana da kuma wasu ikidun kasashen yamma.

ABNA24 : Tashar talabijin na Prestv a nan Tehran ya nakalto kungiyar musulmi mafi girma a Amurka, Council of American-Islamic Relations (CAIR) yana fadar haka. Nihad Awad sakataren kungiyar ya kara da cewa shugaba Macron bai da ‘yencin fadawa musulmi yadda zasu gudanar da addininsu.

A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci majalisar musulmi ta kasar ko ‘French Council of Muslim Worship’ (CFCM) kan cewa ya bawa majalisar makonnin biyu su tsara masa akidun ‘yencin bil’adam da kasashen yamma suke kai wadanda kuma musulman kasar suka amince da su.

Kafin haka dai shugaban ya nuna goyon bayansa ga wata Jaridar kasar mai suna Chalie Ebdo” wacce ta buga zane-zanen batanci ga Manzon Allah (s) sannan jinganawa musulmi wasu mummunan ayyuka. Wanda ya sami gagarumar maida martani a tsakanin musulmi a duk duniya.

342/