18 Nuwamba 2020 - 17:25
Zarif:An Wuce Marhalar Da Amurka Take Tilastawa Kasashen Duniya Bin Ra’ayinta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka bata isa ta tilastawa kasashen duniya ra’ayinta kamar yadda take yi a baya ba.

ABNA24 : Zarif ya bayyana haka ne ga jaridar “Iran” wacce buga hirar da ta yi da shi a safiyar yau Laraba.

Zarif ya ce idan zabebbeb shugaban kasar Amurka Joe Biden yana son samun nasara a shugabancin kasar Amurka to dole ne ya yarda da cewa karfin tattalin arziki na duniya ya koma gabas. Idon kuma ya yi kokarin hana hakan ba zai sami nasara ba.

Daga karshe ministan ya bayyana cewa siyasar Trump ta takurawa kasar Iran don cimma manufarsa bata yi wani amfani ba. Kuma idon Amurka tana son mutuncin kanta, ta girmama kudurori da dokokin kasa da kasa. Daga ciki har da kuduri mai lamba 2231 ta yarjejeniyar Nukliyar kasar Iran. Idan ta yi haka ta kuma dage takunkuman zalunci da ta dorawa kasar Iran, Iran a shirye take da koma kan alkawuran da ta dauka a cikin yarjejeniyar.(19)

342/