11 Nuwamba 2020 - 11:29
Jami’an Pentagon Na Ci Gaba Da Murabus Tun Bayan Da Trump Ya Kori Sakataren Tsaro

Ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon, ta shiga cikin wani yanayi da zaman dar-dar sakamakon ci gaba da murabus din da manyan jami’an ma’aikatar suke yi tun bayan da shugaban Amurkan Donald Trump ya kori sakataren tsaron Amurkan Mark Esper.

ABNA24 : Rahotanni sun ce daga cikin manyan jami’an ma’aikatar tsaron Amurkan da suka yi murabus din sun hada har da babban jami’in tsare-tsare na ma’aikatar James Anderson, babban jami’in bangaren leken asiri na ma’aikatar Joseph Kernan da kuma shugaban ma’aikata na ma’aikatar Jen Stewart.

A shekaran jiya ne dai shugaba Trump din wanda ya ke cikin fushi da damuwar kayen da ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar ya kori sakataren tsaron Amurkan Mark Esper lamarin da wasu manyan jami’an Amurka suka fara nuna damuwarsu kan yanayin da kasar za ta shiga cikin sauran kwanakin da suka saura na gwamnatin Trump din.

Shugaban kwamitin harkokin soji na majalisar Amurkan Adam Smith ya bayyana cewar tun daga lokacin da aka zabi Joe Biden a matsayin zababben shugaban Amurkan, Trump da mabiyansa suka fara haifar da yanayi na dar-dar, lamarin da a halin yanzu ya iso har zuwa ma’aikatar tsaro, wanda ya ce hakan lamari ne mai hatsarin gaske.

Wasu rahotannin ma sun ce shugaba Trump din yana shirin korar shugabar hukumar leken asiri ta Amurka CIA, Gina Haspel.

342/