8 Nuwamba 2020 - 12:22
​Trump Ya Shigar Da Kara A Kotuna 12 Domin Kalubalantar Sakamakon Zabe

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya shigar da kara a kotuna 12 domin kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a kasar.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, Donald Trump ya yi zargin cewa an yi masa magudi ne a zaben shugaban kasa da aka gudanar a Amurka, musamman a jihohin da yake a gaba, daga cikin jihohin da ke fayyace wada ya lashe zabe.

Daga cikin johohin raba gardama da suke fayyace makomar wanda ya lashe zabe wanda Trump bai yarda da ingancin yadda aka kada kuri’a da kuma gudanar da kidayarsu ba akwai Pennsylvania, Arizona, Nevada, da kuma Georgia, inda yake ikirarin cewa an tafka magudi a wadannan jihohi, musamman ma yadda ya kasance a gaba a wasu daga cikinsu, amma daga bisani kuma ya koma baya.

To sai dai wannan zargi na Trump ya jawo rarrabuwar kai hatta a cikin jam’iyyarsa, inda wasu daga cikin kososhin jam’iyyar suke ganin abin da yake fada baban kure ne.

Tsohon dan takarar shugabancin Amurka a Jam’iyyar Republican kuam dan majalisar dattawa a halin yanzu Mitt Romney ya mayarwa shugaba Donald Trump da kakkausan martani, bisa zargin tafka magudi da kuma cewa 'yan Jam’iyyar Democrat na kokarin sace zaben, inda ya ce Trump yana da hurumin gabatar da bukatar sake kidayar kuri’u ko kuma gudanar da bincike dangane da zargin magudin da yake zargin an yi, amma kure ne shi da kansa ya ce an yi magudi ko kuma anyi satar kuri’u a wannan zabe

342/