4 Nuwamba 2020 - 10:50
An Fara Fidda Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na Kasar Amurka

An Rufe runfunan zabe a mafi yawan jihohin Amurka 50 kuma tuni sakamakon zaben ya fara fitowa a wadanan jihohi.

ABNA24 : Masu sanya idodai sun bayyana cewa miliyoyin Amurkawa sun fito don kada kuri’unsu a mafi yawan jihohin.

Ya zuwa yanzun dai kamar yadda sakamakon da tashar talabijin ta Skynews yake yadawa shugaban Trump yana da masu zabe na musamman wato electoral collage 204, a yayinda Joe Biden yake da 223, sai dai har yanzu sakamakon bai kai matsayinda za’a bayyana wanda ya lashe zaben kai tsaye ba.

342/