ABNA24 : Sabon tsarin wanda zai shafi larduna 25 cikin jimillar larduna 31, zai hana dukkan ababen hawa fita daga Lardunansu na asali, sannan zai hana masu zuwa daga wasu larduna shiga wani lardi na daban. Wato zirga-zirgan ababen hawan, zai takaita ne a cikin larduna kadai.
Har’ila yau takaida zirga-zirgan zai fara ne daga yau Litinin har zuwa ranar jumma’a ami zuwa 6 ga watan Nuwamba.
Tashar talabijin ta Presstv ta nakalo kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa Simo Saadat Lara ta na cewa a jiya Lahadi kadai mutane 434 ne cutar ta kashe a duk fadin kasar, sannan wasu 7,719 suka kamu da ita.
342/