ABNA24 : Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, daga cikin mutane kusan 200 da ke cikin kwale-kwalen da ke dauke da su, kusan 60 ne aka iya cetowa, yayin da 140 suka bata a cikin ruwa.
Rahotanni sun ce bakin na bukatar zuwa tsibirin Canary da ke Spain ne lokacin da hadarin ya auku.
Jami’in hukumar Bakary Doumbia ya bukaci taimakon gwamnatoci da kasashen duniya wajen ganin sun dakile mutanen da ke safarar irin wannan mutane da ke neman isa Turai ta kowacce hanya.
Gwamnatin kasar Spain ta ce akalla baki 11,000 suka isa gabar ruwanta a cikin wannan shekara, sabanin 2,557 da aka samu a shekarar da ta gabata.
Hukumar ta ce a wannan shekara mutane 414 suka mutu daga cikin irin wadannan mutane da ke neman tsallakawa Turai.
342/