ABNA24 : Makon hadin kai wanda ake yi a lokacin bukukuwan tunawa da haihuwar manzon Allah ( s.a.w.a), wata dama ce mai matukar muhimmanci domin jaddada ‘yan’uwantaka a tsakanin al’ummar musulmi.
A kowace shekara a Iran ana fara bukukuwan makon hadin kai a tsawon mako guda saboda jaddada hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi.’
Bikin na bana shi ne karo 34 daga lokacin da Imam Khumain ( Q.s) ya assasa shi.
342/